Babban Masallacin Makkah (da larabci; ٱلْـمَـسْـجِـد ٱلْـحَـرَام a furucci; al-Masjid al-Ḥarām a ilimance; Masallaci mai Tsarki, da turanci; The Sacred Mosque)) shine masallacin daya zagaye Kaaba dake birnin Mecca, Saudiya. Wuri ne na ziyara domin aikin hajji, wanda kowane Musulmi dole ya aikata shi, karanci sau daya a rayuwarsa idan yana da ikon zuwa, wanda aikin yahada da kewaye dakin Kaaba dake a cikin masallacin. Kuma nan muhimmin wurin yin ‘Umrah, karamin aikin hajji da akeyi a kowane lokaci a cikin shekara. Babban masallacin yahada da wasu mahimman wurare, wadanda suka hada da, Baƙin Dutse, Rijiyar ZamZam, wurin tsayuwar annabi Ibrahim, da duwatsun Safa da Marwa. A bude Masallacin yake, akowane lokaci da yanayi.
Babban Masallacin harami shine masallaci mafi girma a duniya, kuma anmasa gyararraki da fadada shi a lokuta daban-daban a shekaru. Ta wuce lokuta da dama ƙarƙashin kulawar Halifofi daban-daban, sultans da sarakuna, kuma ayanzu babban masallacin na ƙarƙashin kulawar Sarkin Saudi Arabia wanda shine Custodian of the Two Holy Mosques. Tana nan ne a gaban Abraj Al Bait, mafi tsayin ginin agogo a duniya, aikin gininsa dake cike da cece-kuce akan rushed wuraren tarihi na farkon musulunci da gwamnatin Saudiya tayi.