Tabkin Cadi ko Chadi wani babban tabki ne dake a inda ake kira a yanzu dasunansa wato yankin tabkin chadi, wannan tabki yana a arewa maso gabashin Nijeriya ne tsakanin jihar Borno, Kasar chadi, kasar Kamaru da kasar Nijar, kuma tabkin yakasance mai mahimmanci ga alumman dake wannan kasashe dasuke kewaye da tabkin, a inda yake samar da ruwan amfani ga mutane sama da miliyan 30.
Kimanin girman kasan da tabkin keda shi yakai: 1,350 km2 (520 sq mi) a shekara ta 2005 Zurfin tabkin yafara daga: 1.5 m (4 ft 11 in) zuwa matsanaicin zurfin dayakai 11 m (36 ft) sannan tsawon gabar tabkin yakai 650 km (400 mi)