Masallacin Shitta-Bey masallaci ne da kuma cibiyar koyar da addinin musulunci a Legas. Yana ɗaya daga cikin tsofaffin masallatai a Najeriya. Masallacin yana a filin Martins Ereko, a Tsibirin Legas a jihar Legas, Nijeriya. An kafa shi ne a shekarar 1892, sannan Hukumar kula da kayan tarihi ta Nijeriya ta zaɓe shi a matsayin ginin tarihi a shekarar 2013.