Tabkin Malawi, Anfi saninsa da Tabkin Nyasa a kasar Tanzania da kuma Lago Niassa a kasar Mozambique, nadaga cikin Manyan Tabkunan Afirka kuma itace tabki a mafi kudancin East African Rift system, tana nan ne a tsakanin kasar Malawi, Mozambique da Tanzania.
Itace tabki Mafi girma na hudu mai ruwa maikyau a duniya a fadi da cika, na tara mafi girman tabki a duniya wuri fadi da tsawo, kuma na uku da nabiyu a girma da zurfi a nahiyar Afirka. Tabkin Malawi na dauke da nau'ukan kifaye daban-daban fiye da kowane tabki a duniya, wadanda a kalla yana dauke da nau'uka 700 na cichlids. Bangaren tabkin na Mozambique gwamnatin kasar ta kebeshi a matsayin wurin Adana a ranar 10 ga watan Yunin, 2011, A kasar Malawi bangaren tasu na cikin Lake Malawi National Park.